An kwantar da ɗalibai sama da 100 a asibiti bayan da suka shaƙi gurɓatacciyar iska a jihar Ogun

Sulaiman SaadHausa2 minutes ago



Dalibai sama da 100 daga makarantu daban-daban na sakandare a Ijebu-Ode, Ago-Iwoye da Ijebu-Igbo a Jihar Ogun sun kwanta a asibiti a ranar Laraba sakamakon wani sabon lamarin fitar iskar gas a yankunan.

Rahotanni sun nuna cewa an kwantar da daliban a Asibitin Jiha da ke Ijebu-Ode, Babban Asibitin Ijebu-Igbo da sauran cibiyoyin lafiya bayan sun shaƙi wani wari mai ƙarfi na iska mai cutarwa.

Majiyoyi sun ce makarantun da suka fi fuskantar matsalar sun haɗa da Ijebu-Igbo Girls Grammar School, Anglican Girls Grammar School da ke Ijebu-Ode, da Itamerin Comprehensive High School da ke Ago-Iwoye, da sauransu.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna wasu dalibai suna suma yayin da ake garzayawa da su asibiti bayan sun shaƙi iskar da ke haddasa matsananciyar damuwa, wadda gwamnati ta bayyana tun da farko cewa iskar sinadarin methane ce.

Wani malami daga ɗaya daga cikin makarantun da abin ya shafa ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safe.


“Dalibai da ma’aikata sun fara shaƙar iskar kuma suka fara samun matsalar numfashi. Wasu ma sun suma, daga bisani aka kai su asibiti.” a cewarsa

“An tilasta wa wasu makarantu a Ago-Iwoye rufewa a lokacin karatu da misalin ƙarfe 11 na safe saboda yanayin ya ƙara tsananta kuma ya zama abin wahala. Makarantun da suka fi fama da matsalar sun haɗa da Ijebu-Igbo Girls Grammar School da Anglican Girls Grammar School a Ijebu-Ode.

“Wasu iyaye da suka ji labarin abin da ya faru sun zo suka ɗauki ’ya’yansu domin babu wanda ya san ainihin abin da ke faruwa. Mun kuma ji cewa wannan matsalar fitar iskar tana faruwa tun daga watan Afrilu, tare da kai daruruwan dalibai asibiti duk lokacin da ta bayyana ba zato ba tsammani.

“Dukkanmu muna cikin fargaba game da lafiyarmu da kuma ta dalibanmu. Ina ganin gwamnati tana ɗaukar lokaci mai tsawo wajen gano tushen wannan iskar mai haɗari. Dole ne ta yi gaggawar magance matsalar kafin ta zama bala’i.”

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ne karo na huɗu da wannan fitar iskar gas ke haddasa rudani da tashin hankali a yankin Ijebu.

Lamarin farko a watan Afrilu ya shafi kusan dalibai 40, yayin da sama da dalibai 120 suka kwanta a asibiti bayan wani makamancin haka a watan Mayu. Haka kuma, a ranar 1 ga Yuni, akalla dalibai 69 suka kwanta a asibiti bayan sake wani lamarin fitar iskar, wadda daga baya aka tabbatar methane ce.

Makarantun da abin ya shafa a lokutan baya sun haɗa da Our Lady of Apostles Secondary School da ke Epe Garage, Ijebu-Ode; Anglican Girls Grammar School, Ijebu-Ode; da St. Anthony Grammar School da ke Ijebu-Imusin, da sauransu.



Da aka tuntubi Kwamishinan Muhalli na jihar, Ola Oresanya, a ranar Laraba, ya ce:

“Mun riga mun ɗauki matakan da suka dace kuma muna kula da halin da ake ciki.”

Babban manajan hukumar kare nuhalli ta jihar Ogun, Kehinde Bello, ya kai ziyara wuraren da abin ya shafa a Ijebu-Ode da Ijebu-Igbo domin tantance halin da ake ciki.

Bello ya bayyana cewa sabon lamarin yana da alaƙa da fitar iskar daga ƙarƙashin ƙasa, wanda aka fara lura da shi a Ijebu-Ode tun daga watan Afrilu na shekarar 2026.

Ya ce an shawo kan lamarin, yana mai ƙara da cewa gwamnati za ta nemo mafita mai ɗorewa ga matsalar.

A cewarsa, binciken gwamnati ya nuna cewa wannan al’amari na faruwa ne sakamakon halittar yanayin ƙasa da layukan karkacewar ƙasa da motsin faranti na duniya (tectonic fault lines), ba wai sakamakon ɓarna ko fashewar bututun gas ba.

Bello ya buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa ana sa ran daliban da abin ya shafa za su warke bayan samun kulawar likitoci.

Ya kuma shawarci mutanen da suka kasance cikin wuraren da warin iskar ya shafa da su rufe hancinsu da bakinsu da rigar hannu mai ɗanɗano ruwa maimakon sanya abin rufe hanci (face mask).

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...