

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce jami’anta sun gano wata cibiyar harhaɗa magungunan gargajiya da ake zargin tana aiki ba tare da izini ba a yankin Agege na jihar Legas.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce an gano cibiyar ne bayan wani rahoto da jaridar The Guardian ta wallafa a ranar 10 ga Oktoba, 2026, game da wasu magungunan gargajiya da ke dauke da lambobin rajistar NAFDAC na jabu.
NAFDAC ta ce tawagarta ta bincike ta gudanar da sintiri tare da gano nau’o’i uku na Asheitu Adams Bitters masu dauke da lambar rajista A7-1827L.
“Bincike ta hanyar dandalin NAPAMS na NAFDAC ya nuna cewa wannan lambar rajista ta asali mallakin maganin tari na Greentol Cough Syrup ce, wanda hakan ke tabbatar da cewa an yi amfani da ita ta hanyar yaudara a kan wadannan magungunan gargajiya,” in ji sanarwar.
“Hukumar ta kuma bayyana cewa Babban Darakta kuma Shugaban Kamfanin bai kasance a wurin lokacin da aka gudanar da samamen ba, yayin da aka kama manajan kamfanin domin ci gaba da yi masa tambayoyi.”
Wannan ganowa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da NAFDAC ta gano wata cibiyar kera barasa ta jabu da ake zargi a jihar Abia.