
Hukumomin Italiya sun yi watsi da bukatun neman mafaka na ’yan Najeriya 2,220 a shekarar 2025, yayin da jimillar ’yan Najeriya 3,385 suka nemi mafaka a kasar a wannan shekarar.
Rahoton Asylum Information Database (AIDA) 2025 kan tsarin neman mafaka a Italiya, wanda aka tattara bayanansa daga hukumomin kasar da Hukumar Tarayyar Turai mai kula da mafaka, ya bayyana cewa an yanke hukunci kan shari’o’in ’yan Najeriya 3,390.
Daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci, an bai wa ’yan Najeriya 660 cikakken matsayin ‘yan gudun hijira, yayin da wasu 55 suka samu kariya ta musamman ga wadanda ke fuskantar barazana mai tsanani. Haka kuma, an bai wa mutane 460 kariya ta musamman karkashin dokokin Italiya.
Jimillar ’yan Najeriya 1,175 ne suka samu wani nau’in kariya, wanda ya kai kashi 34.66 cikin 100 na shari’o’in da aka yanke wa hukunci. Wannan ya haura matsakaicin kaso na kashi 30 da Italiya ta samu a dukkan kasashe.
Rahoton ya kuma nuna cewa, ya zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025, akwai wasu bukatun neman mafaka na ’yan Najeriya 4,120 da har yanzu hukumomin Italiya ba su yanke wa hukunci ba.
A shekarar 2025, Italiya ta samu bukatun neman mafaka 126,635, adadin da ya ragu idan aka kwatanta da 151,120 da aka samu a shekarar 2024. Haka kuma, rahoton ya nuna cewa yawan mutanen da suka samu kariya ya ragu daga kashi 35 a shekarar 2024 zuwa kashi 30 a 2025.
A watan Oktoban 2024, Kotun Tarayyar Turai ta soke tsarin da Italiya ke amfani da shi wajen ayyana wasu kasashe a matsayin wuraren da ake ganin ba su da hadari, lamarin da ya sa aka cire Najeriya daga jerin kasashen. A baya, wannan matsayi kan sanya bukatun mafaka daga ’yan Najeriya cikin tsarin tantancewa cikin gaggawa.