Jami’an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna.
Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan shekara 30 na zaune ne a yankin Yan Bokolo a Malalin Gabas dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Jami’an ƴan sandan rundunar Operation Yaƙi su ne suka kama shi a ranar 21 ga watan Mayu biyo bayan bayanan sirri da suka samu daga Sashen Bayanan Sirri na hedkwatar rundunar ƴan sanda dake Abuja.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda aka kaman na da alaƙa da Dogo Haliru gawurtaccen mai garkuwa da mutane da aka sani da addabar jihohin Zamfara,Katsina da kuma babbar hanya hanyar Abuja zuwa Kaduna.