Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Juma’a ta ce ta kashe wani da ake zargin dan fashi da makami ne a wata fafatawa, yayin da aka kama wasu uku, sannan shida suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Sharif Saad, ya ce an sanar da sashen kula da rundunar ‘yan sandan cewa wasu gungun ‘yan fashi da makami da suka kware wajen addabar al’ummar garin Gombe, musamman a kwatas-kwatas ɗin Arawa, Malam Inna da Nayi Nawa.
Wani bangare na bayanin Saad ya kara da cewa, “’yan fashin sun kai farmaki gidan Alhaji Gidado Muhammad Sani da ke unguwar Arawa, inda suka yi ta harbe-harbe tare da yi musu fashin dukiyoyinsu.”