Ƴan sanda sun kama riƙaƙƙen ɓarawon awaki a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin barawo ne da ya kware wajen satar awaki a kauyen Pasali Konu da ke karamar hukumar Kagarko a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Lahadi a Kaduna cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar.

Hassan ya ce, a ranar 11 ga watan Nuwamba da misalin karfe 0430, wata tawagar sa ido da ‘yan banga, yayin da suke aikin sintiri a kauyen, sun kama matashin mai shekaru 20 da haihuwa.

A cewarsa, wanda ake zargin ya fito ne daga kauyen Igwa na karamar hukumar Kagarko.

“Wanda ake zargin, wanda ya kware wajen satar awaki, ya amsa cewa su biyu ne da suka zo kauyen domin satar awaki,” in ji Hassan.

More from this stream

Recomended