Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suka Kashe Dan Acaba a Bauchi

Ƴan sandan jihar Bauchi sun kama wasu mutane biyu da ake zargin sun kashe wani ɗan acaba mai suna Muhammad Tukur daga garin Kangere a karamar hukumar Bauchi da ke jihar wanda aka taba bayar da sanarwar ya bata.

Wadanda ake zargin Hashimu Adamu mai shekaru 22 da Anas Muhammed mai shekaru 23 ne suka dauki marigayin don ya kai su zuwa kauyen Badaqoshi da ke karamar hukumar Alkaleri.

An ce sun daba masa wuka a ciki lokacin da suke kan hanya, inda suka gudu da babur din sa mai kirar Bajaj.

Babban yayansa ne ya bayyana cewa ya ɓata, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana wa manema labarai a Bauchi.

More from this stream

Recomended