Premier League: Liverpool na ci gaba da jan zarenta

Sadio Mane a kwallon da ya zira wa Villa
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Liverpool ta saba zira kwallo a mintinan karshe

Liverpool ta samu nasarar doke Aston Villa har gida da ci 2-1 bayan kwashe kusan minti 93 ana fafatawa.

Tun da fari Trezeguet ne ya ci wa wa Aston Villa a minti na 21 da fara wasan, yayin da Andy Robertson ya farke wa Liverpool kwallonta a minti 87.

Ana gab da tashi daga wasan ne kuma Sadio Mane ya kara ta biyu, wadda da ita ne Liverpool ta ci gaba da zama a saman teburi.

Har yanzu dai Liverpool ce ke ci gaba da jan ragamar gasar Premeir da maki shida tsakainta da Manchester City da ke biye mata.

Liverpool dai na yawan samun nasarar jefa kwallo bayan minti 90 da fara wasa. Kwallon da Sadio Mane ya ci ita ce ta 35 da kungiyar ta ci bayan cikar minti 90 na wasa, sama da kowace kungiya kenan a Premier da kwallo 10.

Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City ne a wasa na gaba kafin daga bisa ni ta je Crystal Palace, inda ake ganin wadannan wasanni a matsayin wadanda za su kawo wa Livepool kalubale.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...