Kevin de Bruyne: Ɗan wasan tsakiya na Manchester City ya kamu da Covid-19

Kevin de Bruyne celebrates scoring for Belgium

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Kevin de Bruyne scored for Belgium on Tuesday

Dan wasan tsakaiya na Manchester City evin de Bruyne gwaji ya tabbatar da ya kamu da cutar korona bayan ya dawo daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa.

Ɗan wasan mai shekara 30 ya killace kansa na tsawon kwana 10, wanda hakan ke nufin ba zai buga wasan da Manchester City za ta kara da Everton ba a ranar Lahadi da kuma karawar gasar zakarun Turai da Paris St-Germain.

De Bruyne, wanda aka yi allurar rigakafin korona, ya ci wa Belgium ƙwalli a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya ƙasarsa ta fafata da Wales a ranar Talata.

“Muna fatan alamomin ba su yi muni ba,” in ji kocinsa Pep Guardiola.

“Ba za a daɗe ba zai dawo, ba za mu damu da irin girman giɓin da muka samu ba. Yana da muhimmanci sosai. Dole mu taimaka masa kuma muna fatan zai samu sauƙi a yayin da ya killaci kansa.”

(BBC Hausa)

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...