Mun kashe miliyan 500 don samar da banɗakai—Gwamnatin Jigawa

Gwamnatin Jigawa ta ce ta kashe naira miliyan 500 wajen samar da ingantattun wuraren wanka a makarantu da asibitoci da kasuwanni da wuraren ajiye motoci a fadin jihar.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Ibrahim Hannungiwa, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Dutse, ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakai masu inganci don tabbatar da ɗorewar shirin.

A cewar Hannungiwa, jihar na shirin zarce burin ODF na kasar nan da shekarar 2025.

Hannungiwa ya ce an samu nasarar hakan ne ta hanyar yin kokari sosai ta hanyar aiwatar da manufofi da tsare-tsare masu inganci tare da hadin gwiwar ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Kwamishinan ya kara da cewa jihar ta kafa wani kwamiti da zai tsara hanyoyin da za a bi domin ɗorewar matsayinta na ODF ta hanyar tabbatar da kawar da wannan barazana gaba daya.

More from this stream

Recomended