
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta gano wani gida a Legas da ake zargin ana amfani da shi wajen ajiye kwalaben giya da aka shirya sake amfani da su wajen ƙera giya ta jabu.
Hukumar ta ce ta gano kwalabe sama da buhu 100 a wani gida da ke lamba 322B, kan titin Meiran Road, Agbado, Oke Odo. An lalata kwalaben domin hana sake amfani da su wajen samar da giyar jabu.
Mataimakin daraktan sashen bincike da tabbatar da bin doka na hukumar, Kunle Ojo, ya ce an gano wurin ne bayan samun sahihan bayanan sirri. Ya bayyana cewa ana wanke kwalaben ne domin samar da su ga mutanen da ake zargin suna ƙera giya ta jabu.
NAFDAC ta yi kira ga jama’a da su sanar da ofishinta mafi kusa idan sun gano wasu ayyukan da ake zargi da saɓa wa doka a yankunansu.
Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta kai samame wasu shagunan ɓoye sama da 20 a kasuwar baje kolin kasuwanci ta ƙasa da ke Ojo, Legas, a ranar 13 ga Oktoba, inda ta ƙwace giya ta jabu da wasu abubuwan sha da suka ƙare wa’adin amfani.