
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu bisa zargin ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar, yana mai cewa hakan na kaucewa ɗaukar alhakin manufofin gwamnatinsa.
Atiku, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya ce ’yan Najeriya na da haƙƙin neman bayani kan hauhawar farashin kayayyaki, talauci, matsalar tsaro da yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati.
Ya kuma yi tambayoyi kan cire tallafin man fetur, faɗuwar darajar naira da wasu manyan kuɗaɗen da aka rubuta a cikin kasafin kuɗin ƙasa, yana kira ga gwamnati da ta bayyana yadda aka kashe su da sakamakon da aka samu.
Atiku ya kuma danganta matsin tattalin arzikin da matsalar tsaro, inda ya buƙaci gwamnati ta yi bayani kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma korar al’umma daga muhallansu.
Ya ce ya kamata a auna aikin gwamnati bisa nasarorin da ta samu wajen inganta rayuwar jama’a, maimakon ɗora laifi kan ’yan adawa.