
Rundunar ’yan sandan jihar Delta ta ce ta kuɓutar da wani matashi mai shekaru 23 da aka yi garkuwa da shi, tare da kama mutane takwas da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a ayyukan da aka gudanar tsakanin 20 zuwa 23 ga Oktoba, 2026.
Kakakin rundunar, SP Bright Edafe, ya ce an yi garkuwa da matashin ne a ranar 19 ga Oktoba a Owa-Alero, inda aka ɗauke shi daga gaban gidansa zuwa wani daji. Bayan samun rahoto daga ɗan’uwansa, ’yan sanda tare da taimakon masu sa-kai suka gudanar da bincike tare da kuɓutar da shi washegari. Ana ci gaba da neman waɗanda suka tsere.
A wani samame da aka kai wani otal a Abraka, an kama mutane shida da ake zargi da ayyukan ƙungiyar asiri, tare da ƙwato bindiga da wasu abubuwan da ake zargin tabar wiwi ne.
Haka kuma, jami’an rundunar sun kai samame gidajen wasu mutum biyu a yankin Ekuku-Agbor, inda suka kama su tare da ƙwato bindigogi da harsasai. Jimillar kayayyakin da aka ƙwato a ayyukan sun haɗa da bindigogi uku, harsasai 26 da abubuwan da ake zargin tabar wiwi ne.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Samuel Erale, ya ce rundunar za ta ci gaba da ayyukan da suka dogara da bayanan sirri domin dakile laifuka da kare al’umma. Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suke zargi ga jami’an tsaro.