Mayakan Boko Haram sun harbe sojoji 6

Rahotanni na nuni da cewa mayakan Boko Haram sun kashe a kalla sojoji shida a wani hari kan sansanin sojoji dake kauyen Kareto a karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

Yan ta’addar dake kan babura sun farma sansanin sojan da misalin karfe 7 na daren ranar Alhamis.

Harin na ranar Alhamis na zuwa ne kasa da wata guda bayan da mayakan suka kashe jami’an soja sama da 25 lokacin da suke tsaka da sauyawa mutanen wani kauye matsuguni.

Wata majiya ta fadawa jaridar The Cable cewa mayakan na Boko Haram sun shafe sama da sa’o’i uku suna musayar wuta da sojojin a harin na ranar Alhamis.

A cikin wadanda aka kashe a farmakin akwai kwamandan bataliya ta 158 ya yin da wasu daga cikin sojojin ba a san halin da suke ciki ba har ya zuwa lokacin da jaridar ke hada wannan rahoto.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...