Majalisar Kolin Harkokin Shari’ar Musulunci Ta Najeriya Ta Kalubalanci Shekau | VOA Hausa

A wani taron manema labarai da majalissar ta kira a Kaduna game da barazanar da Shekau ya yi a faifan bidiyon da ya fitar ta cewa lokaci ya yi da ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farga.

Daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci a Najeriya, Sheik Abdulwahab Abdullahi Mohammad, ya kalubalanci Shugaban Kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau game da faifan bidiyon da ya fitar cewa har in ya cika jarumi, to ya fito yayi gaba-da-gaba da jami’an tsaro.

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da batun matsalar tsaro a Najeriya yake dada jan hankalin ‘yan kasa masamman ganin irin barazanar tsaron da aka fuskanta a kasar cikin wannan wata na Fabarairu.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...