Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da jakar da ta bata mai dauke da sama da Naira miliyan 100.

A ƙarshen taron wa’azi na musamman da aka gudanar a Bauchi, Daraktan kungiyar Agaji ta farko na kasa Engr Mustapha Imam Sitti ya yabawa Kankia bisa gaskiyarsa.

Kungiyar JIBWIS reshen jihar Bauchi ta bayyana a shafinta na sada zumunta na Facebook cewa Kankia ya gano jakar kuma ba tare da bata lokaci ba ya kai rahoto ga ‘yan sanda. 

Mai shi ya tabbatar da cewa babu abin da ya ɓace a cikin kuɗin.

Bisa la’akari da gaskiyarsa, kungiyar Izala ta karrama Kankia da lambar yabo da kuma daukar nauyinsa a  aikin hajjin bana.

Ya kuma karbi Naira miliyan biyu daga hannun Hon.  Abdulmalik Zannan Bangudu da motar bas daga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed domin fara harkar kasuwanci.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...