Shugabannin Izala sun kama hanyar Kebbi domin gabatar da jana’izar Sheikh Giro

Shugabannin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatis Sunna a Najeriya sun kama hanyar Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar domin gabatar da jana’izar marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.

Ƙungiyar ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook.

Sanarwar ta ce: “Shugabanin IZALA sun tashi zuwa Birnin kebbi Domin halartan Janaza

“Shugaban JIBWIS Sheikh Bala Lau, da Shugaban Malamai Sheikh Dr. Jalo jalingo, sakataren kungiya Sheikh Kabiru Gombe, Sakataren tsare-tsare na majalisar agaji Sheikh Salisu Gombe. Sakataren marayu na kasa Alhaji Usman da sauran tawaga sun tashi zuwa Birnin kebbi domin samun janazan Sheikh Giro Argungu a garin Argungu. Allah ya sauke su lafiya. Amin”

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...