Sarkin Musulmi ya ce an ga watan Ramadan a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Litinin 11 ga Maris, 2024, a matsayin 1 ga watan Ramadan.

Sanarwar ta zo ne biyo bayan ganin watan a sassa daban-daban na Najeriya a ranar Lahadi, wanda ke cika kwanaki 29 ga watan Sha’aban.

A wata sanarwa da ya fitar, Sultan Abubakar ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne bisa rahotannin da shugabannin Musulmin kasar suka bayar na tabbatar da ganin watan.

Ya bukaci al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara azumin ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

More from this stream

Recomended