Connect with us

Hausa

Hotunan bikin ranar demokradiyya a Najeriya

Najeriya ta yi bikin ranar Demokradiyya ran 12 ga Yuni, don tunawa da sahihin zabe na farko da aka fara yi a kasar ran 12 ga watan Yunin 1993, shekaru goma bayan mulkin soja.

Ga wasu daga cikin hotunan abubuwan da suka faru a lokacin bikin.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari da Mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa Dolapo Osinbajo da sabon Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da sauran manyan baki a wajen bikin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Daya daga cikin masu nishadantar da mutane a lokacin da take taka rawa a Dandalin Eagle Square da ke birnin Abuja.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a lokacin da ake tuka shi a mota inda ya ke duban masu faretin girmamawa a Dandalin Eagle Square.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron bikin ranar demokradiyyar har da ‘yan kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Faretin ‘yan sanda a lokacin bikin ranar demokradiyya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yana gaisawa da shugaban Rwanda Paul Kagame a lokacin bikin. Daga bayansu kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya ne Ken Nnamani da wasu manyan baki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu sojoji suna fareti a gaban Shugaba Muhammadu Buhari yayin da shi kuma yake kallonsu a Dandalin Eagle Square a lokacin bikin.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Wasu ‘yan rawa suna nishadantar da ‘yan kallo a filin da aka gudanar da bikin a Abuja.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake jawabi a Dandalin Eagle Square.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar adamu yana sara wa Shugaba Muhammadu Buhari.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mutane sama 100 ne ke neman Ganduje ya nada su kwamishinoni

Mutane sama da 100 ne da suka hada da malaman manyan makarantu,yan siyasa da kuma kwararru ke hankoran darewa gurbin kujerar kwamishina a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa yan siyasar dake neman mukamin sun fito ne daga bangarorin siyasa daban-daban da suka hada da tsagin tsohon gwamna,Malam Ibrahim Shekarau, tsagin tsohon mataimakin gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar da kuma tsagin tsohon shugaban hukumar lura da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, Aminu Dabo.

Wata majiya dake kusa da gwamnatin ta fadawa jaridar cewa kaso 40 ne kacal cikin tsofaffin kwamishinonin ake sa ran za su sake dawowa kan mukamansu.

Majiyar da ta nemi a boye sunanta ta bayyana kaso 60 na tsofaffin kwamishinonin ba za su dawo ba bayan da suka gaza yin kokari a lokacin zangon farko na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Sojin Najeriya ne ke kawo tsaiko a yaki da Boko Haram – Buratai

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Boko Haram ta kashe mutum 30 a Konduga ranar Lahadi. Akwai hotuna masu tayar da hankali

Hafsan sojojin kasa na Najeriya ya dora alhakin tsaikon da ake da ake samu a yakin da kasar ke yi da ta’addanci ga sojojin kasar da ke fagen daga.

Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi sojojin da rashin mayar da hankali domin kare kasar a dukkan ayyukan da umarce su da su yi, lamarin da ya ce abin takaici ne.

“Magana ta gaskiya ita ce za a iya alakanta duk wani koma-baya da muka samu a baya-bayan nan a ayyukan da muke yi da rashin mayar da hankali da nuna kaimi wurin bin umarnin da aka bayar ko ayyukan da aka tsara”.

A takaice za a iya alakanta hakan da rashin nuna halin ko-in-kula da dakarun da suke filin daga suke nunawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito shi yana cewa a wurin wani taron ranar Talata.

Sai dai wani jami’in soji ya shaida wa BBC cewa kalaman na shugaban nasu “ba su da tushe, yana mai cewa idan ba a yaba musu ba, to bai kamata a tsine musu ba”.

Fiye da shekara 10 ke nan dakarun Najeriya na fafatawa da mayakan Boko Haram a arewa maso Gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 30,000, yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhallansu.

Janar Tukur Buratai ya shafe shekara hudu yana jagorantar rundunar sojin Najeriya

Manyan jami’an sojoji da kanana da dama sun rasa rayukansu a yakin, wanda gwamnati da sojoji suka ce sun ci karfinsa.

Sai dai har yanzu kungiyar na kai hare-hare, inda ko a ranar Lahadi sai da suka kashe mutum 30 a wani harin kunar bakin-wake, yayin da wasu 40 suka jikkata.

Masu sharhi na ganin irin wadannan kalamai na nuna gazawa ne daga bangaren shugabannin sojin, wadanda wasu da dama suke zarga da kasa yin katabus wuirn kawo karshen kungiyar ta Boko Haram duk da makudan kudaden da ake ware musu.

Baya ga Boko Haram, Najeriya na fuskantar matsalar ‘yan bindiga a arewa maso Yamma da masu satar mutane domin karbar kudin fansa a sassan kasar daban daban.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Yan bindiga sun kona gidaje 21 a wani ƙauye dake Kaduna

Wasu yan bindiga a ranar Litinin sun kai farmaki kauyen Kikuba dake Gundumar Chawai a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna inda suka cinnawa gidaje 21 wuta dake yankin.

Yan bindigar sun isa Yankin suna harbin kan me uwa da wabi da misalin karfe 06:30 na yammacin ranar Litinin a cewar hakimin yankin Yahaya Muhammad.

Jaridar ta gano cewa kauyen na da makotaka da jihar Plateau.

Hakimin na Chawai wanda ya kasance a garin Kaduna domin ganawa da kwamishinan ƴansandan jihar shine ya bayyana wa jaridar Daily Trust abin da ya faru a wata tattaunawa.

Ya ce yan bindigar sun kuma kai farmaki kauyen unguwar Rimi inda suka kashe wasu samari uku a ranar da suka kai hari kauyen Kikuba.

“Sun kai farmaki Kikuba da misalin karfe 06:00 na yamma ranar Litinin a garin dake iyakar Kaduna da Plateau. Kauyen na karkashin Gundumar Chawai akalla gidaje 21 aka kone ya yin da mutum guda ya rasa ransa a harin.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: