Gwamnatin Tarayya za ta fara rabawa É—alibai bashi daga watan Satumba

Gwamnatin tarayya ta ce tana nan tana tsara hanyoyin da za abi domin raba bashin da za a bawa dalibai daga watan Satumba.

David Adejo, babban sakataren ma’aikatar ilimi shi ne ya sanar da haka lokacin da yake amsa tambayoyin yan jarida a Abuja.

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bawa dalibai bashin biyan kuÉ—in makaranta ba tare da sun biya kudin ruwa ba.

Adejo ya ce tsarin zai bawa É—alibai yan Najeriya damar saukin samun ilimin gaba da sakandare ta hanyar cin bashi daga asusun Nigeria Education Loan Fund.

Babban sakataren ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar kowane dan Najeriya ya samu damar samun ilimin gaba da sakandare.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...