
Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya soki matsayar Shugaba Bola Tinubu cewa karɓar bashi ba cutar kuturta ba ce, inda ya bayyana cewa illar bashin da ƙasa ke ci gaba da karɓa ta fi ta kuturta muni, domin tana iya shafar rayuwar al’ummomi da dama, har da waɗanda ba a haifa ba tukuna.
Obasanjo, wanda a lokacin mulkinsa tsakanin 1999 da 2007 ya jagoranci samun rangwamen bashin Paris Club na dala biliyan 30 ga Najeriya, ya ce yayin da kuturta ke shafar mutum guda, yawan bashi yana jefa makomar tsararraki gaba ɗaya cikin haɗari.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a taron shekara-shekara na uku na Ajibosin, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta, Jihar Ogun.
Taken taron shi ne: “Amfani da Fasahar Basirar Ɗan Adam wajen Magance Matsalolin Al’umma da Gaggauta Ci gaban Ƙasa”.
Tinubu ya taɓa bayyana cewa karɓar bashi ba cutar kuturta ba ce, yana mai cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tuƙuru domin biyan duk bashin da ta karɓa.
Sai dai Obasanjo ya soki wannan hujja, inda ya kira ta da maganar banza, tare da nuna damuwa kan yadda bashin ƙasar ke ƙaruwa da kuma yadda shugabanni ke tafiyar da tattalin arziƙin Najeriya.
Haka kuma, ya soki manufofin Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), yana mai cewa ba a tsara waɗannan cibiyoyi ne domin inganta ci gaba da wadata a Najeriya ba.
Ya ce ƙasashen Afirka ba su kamata su riƙa amincewa da duk shawarwarin waɗannan cibiyoyi ba tare da la’akari da yanayin ƙasashensu ba.
Obasanjo ya yi misali da yadda wasu ƙasashe ke tallafa wa harkar noma, alhali Bankin Duniya da IMF ke adawa da tallafin noma a ƙasashe masu tasowa.
Ya kuma yi tambaya kan yadda darajar naira ta faɗi a cikin shekaru 47, inda ya ce a lokacin da ya fara aikin gona, naira ɗaya tana da darajar dala ɗaya da cent 85, amma yanzu ana musayar dala ɗaya kan kusan naira 1,500.
“Me Najeriya ta yi a cikin shekaru 47 da ya sa darajar kuɗinmu ta kai wannan matsayi? Me shugabanninmu suka sani, kuma me ba su sani ba? Daga cikin abin da suka sani, me za su iya yi mana?
“Duk wanda ya ce bashi ba cutar kuturta ba ce, yana faɗin maganar banza ne. Bashi ya fi kuturta muni, domin kuturta tana lalata mutum guda ne, amma bashi yana lalata tsararraki,” in ji shi.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yi gargaɗi kan yadda ake rungumar fasahar basirar ɗan Adam (AI) da sauran sabbin fasahohi ba tare da fahimtar illolinsu ba.
Ya ce ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya na iya amfani da waɗannan fasahohi wajen cin gajiyar ƙasashen Afirka idan har nahiyar ba ta mallaki ikon sarrafa su ba.
Obasanjo ya jaddada cewa Najeriya ce ya kamata ta tsara yadda za ta yi amfani da fasahar AI domin biyan buƙatun ci gabanta, maimakon barin ƙasashen waje su riƙa tsara mata alkiblar fasaha da tattalin arziƙi.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani abu da mutum ko ƙasa ba ta da ikon sarrafa shi, ana iya amfani da shi wajen cutar da ita.
Da yake gabatar da jawabi a wajen taron, wani masani kan tarihi kuma mai sharhi kan siyasa, Dakta Umar Ardo, ya yi gargaɗin cewa Afirka na iya fuskantar sabon salon cin moriyar tattalin arziƙinta ta hanyar fasahar AI idan ba ta mallaki bayananta, kayayyakin more rayuwar fasaha da haƙƙin mallakar fasaha ba.
Ardo ya ce duk da irin damar da AI ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa, amfani da ita ba tare da mallaka, matakan kariya da ƙwarewar cikin gida ba, na iya ci gaba da jefa Afirka cikin tsarin dogaro da ƙasashen waje.
Ya kwatanta hakan da yadda a zamanin cinikin bayi aka riƙa fitar da ’yan Afirka zuwa ƙasashen waje, sannan a zamanin mulkin mallaka aka riƙa kwashe albarkatun ƙasa, yayin da ƙasashen waje ke sarrafa fasahar da ake amfani da ita.
A cewarsa, har yanzu wannan tsari yana ci gaba, domin ƙasashen Afirka na fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su zuwa kayayyakin da za su fi amfani ga tattalin arziƙinsu ba.
Ya kawo misalin yadda Najeriya ke fitar da ɗanyen mai, amma take dogaro da kayayyakin man fetur da aka tace a ƙasashen waje, haka kuma ƙasashen da ke noman koko ke dogaro da masana’antun waje wajen samar da cakulan.
Ardo ya kuma bayyana cewa bayanan da al’ummar Afirka ke samarwa a gonaki, asibitoci, harsuna, kasuwanci da hukumomin gwamnati na ƙara samun daraja, amma galibin cibiyoyin sarrafa bayanai, samfuran AI, haƙƙin mallakar fasaha da ribar da ake samu suna hannun ƙasashen waje.
Ya ce dole ne Afirka ta yi nazari kan yadda za ta shiga wannan sabon zamani na fasaha domin kada ta sake zama tushen albarkatun da wasu za su riƙa sarrafawa tare da cin moriyar ribarsu.