
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a kisan wani jami’in soja, Kofur Benjamin Jige, wanda wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka daba wa wuka har ya mutu.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce hadin gwiwar jami’an ’yan sanda da sojoji ne suka gudanar da samamen tare da kama wadanda ake zargin.
Sanarwar ta ce a ranar 1 ga Nuwamba, 2026, tawagar jami’an tsaro karkashin jagorancin Kyaftin Useini Ariyo ta kai samame otal din New Legit bisa sahihan bayanan sirri domin cafke wadanda ake zargi da hannu a kisan jami’in sojan.
Mutanen da aka kama su ne Godwin Tanko mai shekaru 42, Abuchi Simon mai shekaru 27, Divine Omegle mai shekaru 32 da Samuel Alonge mai shekaru 21.
Rundunar ta kara da cewa bincike ya gano wasu karin wadanda ake zargi, ciki har da wani shugaban kungiyar asiri ta Vikings da aka fi sani da Bigi Rasta, da kuma Simon Joshua Junior, wadanda suka tsere daga wurin da lamarin ya faru.
Ta ce ana ci gaba da farautarsu ta hanyar bin diddigi da binciken dazuzzuka.
Rundunar ta bayyana cewa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Lafia ne ke gudanar da bincike kan lamarin.