
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da sakin kwantena 98 daga cikin 300 da ke ɗauke da kayan aikin wutar lantarki da suka kwashe sama da shekaru 20 a makale a tashoshin jiragen ruwa na ƙasar.
Babban Kwanturolan hukumar, Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Apapa, Legas, yayin ƙaddamar da aikin fitar da kayan aikin daga tashoshin jiragen ruwan.
Ya ce kayan da ke cikin kwantenan sun haɗa da manyan tiransifoma, wayoyin lantarki, na’urorin sarrafa wutar lantarki da sauran kayayyakin da ake buƙata wajen inganta tsarin rarraba wutar lantarki.
A cewarsa, wasu daga cikin kayayyakin da aka shigo da su domin manyan ayyukan wutar lantarki sun kwashe tsakanin shekaru 14 zuwa 20 ba tare da an fitar da su daga tashoshin jiragen ruwa ba.
Adeniyi ya bayyana cewa bayan Ministan Wutar Lantarki ya gabatar da rahoto a taron Majalisar Wutar Lantarki ta Tarayya, Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta sakin kayayyakin tare da warware duk wasu matsalolin kuɗaɗen caji da na gudanarwa da suka hana fitar da su.
Ya ce bisa umarnin shugaban ƙasar, hukumar ta fara aikin sakin sama da kwantena 200, inda aka fara da kwantena 48 daga tashar ENL, sannan za a fitar da wasu 50 daga tashoshin Tin Can da sauran wurare.
Ya ƙara da cewa hukumar na aiki tare da Ma’aikatar Wutar Lantarki, Kamfanin TCN, Niger Delta Power Holding Company, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki domin kammala aikin cikin gaggawa.
Adeniyi ya ce an tanadi matakai na musamman domin sauƙaƙa fitar da kayayyakin, ciki har da ba su fifiko wajen tantancewa, ware jami’an bincike da kuma amfani da rangwamen kuɗaɗen da aka amince da su.
Ya bayyana cewa ƙwararrun ma’aikata za su duba kayayyakin domin tantance waɗanda har yanzu za a iya amfani da su. Za a tura masu amfani zuwa ayyukan da ake gudanarwa da kuma waɗanda ake shirin farawa, musamman a layukan watsa wutar lantarki da tashoshin rarraba ta. Amma za a zubar da waɗanda suka tsufa bisa ƙa’idojin da ake da su.
Ya kuma yaba wa Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, bisa amincewa da rangwamen kuɗaɗen cajin da aka tara kan kayayyakin.
Babban jami’in ya zargi wasu ’yan kwangila da shigo da kayan aikin gwamnati tare da barinsu a tashoshin jiragen ruwa, duk da cewa an ba su kwangiloli kuma an ware kuɗaɗen gudanar da ayyukan.
Ya ce irin wannan hali yana hana ’yan Najeriya samun wutar lantarki, ayyukan yi da sauran amfanin da aka tsara ayyukan za su samar. Ya kuma bayyana ’yan kwangilar da suka karɓi kuɗin gwamnati amma suka gaza kammala ayyukansu a matsayin masu aikata zagon ƙasa ga tattalin arziki.
A nasa jawabin, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce an shigo da kayayyakin ne domin faɗaɗa hanyoyin watsa wutar lantarki, rage cunkoso a tashoshin rarraba ta da kuma ƙara ƙarfin samar da wutar lantarki ga al’umma.
Adeniyi ya yi kira ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ke da kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa da su tuntubi Hukumar Kwastam domin kada kayayyakin da ake buƙata wajen ayyukan ci gaban ƙasa su ci gaba da zama a makale.