Zan Yi Murabus Idan Najeriya Ba Ta Samu Ci Gaba Cikin Shekara Ɗaya Ba Na Mulkin Atiku – Amaechi



Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya ce zai yi murabus daga muƙaminsa idan ’yan Najeriya ba su fara ganin sauyi mai kyau a ƙasar cikin shekara guda da jam’iyyar ta karɓi mulki ba.

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na NewsCentral ranar Juma’a, inda ya yi bayani kan manufofin tattalin arzikin da jam’iyyar ke shirin aiwatarwa gabanin zaɓen 2027.

Ya ce ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya san halinsa, kuma ba zai yi shakkar barin gwamnati ba idan ya ga ba ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Da aka tambaye shi ko da gaske zai yi murabus daga muƙamin mataimakin shugaban ƙasa idan gwamnatin Atiku da Amaechi ta gaza, ya amsa da cewa, “Tabbas. Ba wasa nake yi ba.”

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin da Atiku zai jagoranta za ta samu karɓuwa a wajen ’yan Najeriya cikin shekararta ta farko. A cewarsa, mutane za su yaba wa shugabancinsa tare da yin nadamar rashin zaɓensa a baya.

Dangane da tattalin arziki, Amaechi ya ce ADC na shirin bullo da wani tsari da ta kira tallafin samar da mai, inda za a bai wa matatun mai na cikin gida ɗanyen mai a farashin da bai kai na kasuwar duniya ba, domin rage farashin man fetur.

Ya bayyana cewa dole ne matatun da suka amfana da wannan tallafi su rage farashin man da suke sayarwa ga jama’a. Idan ba su yi hakan ba, za su sayi ɗanyen man ne a farashin kasuwar duniya ba tare da samun tallafin ba.

A bangaren noma, ya ce jam’iyyar za ta sake duba manufofin noma na ƙasar, ta ƙarfafa gwiwar manoman Najeriya tare da rage dogaro da shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa zuba jari a harkar noma zai samar da ayyukan yi da arziki, wanda a ganinsa zai taimaka wajen rage matsalar rashin tsaro.

Haka kuma, Amaechi ya ce ADC ba za ta dakatar da harkokin siyasa da kamfen ɗinta na zaɓen 2027 ba duk da hukuncin kotu da ya shafi rikicin shugabancin jam’iyyar.

Rikicin ya samo asali ne bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, da kuma bayyanar tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban kwamitin riƙon ƙwarya. Sai dai Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, ya ƙalubalanci wannan sauyin, yana mai cewa kundin tsarin jam’iyyar ya ba shi damar maye gurbin Nwosu.

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya goyi bayan ƙarar Gombe, inda ya ayyana kwamitin riƙon ƙwaryar da David Mark ke jagoranta a matsayin wanda bai halatta ba. Kotun ta kuma soke matakan da kwamitin ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.

Sai dai ADC ta ƙi amincewa da hukuncin, tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara. A ranar Juma’a, jam’iyyar ta sanar da shigar da ƙara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin, inda ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kada ta ɗauki wani mataki har sai an kammala shari’ar.

Duk da haka, jam’iyyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da shirye-shiryenta na siyasa da kamfen ɗin zaɓen 2027.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...