
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani jami’in tsaro tare da sace matar aure a harin da suka kai al’ummar Ribah, da ke ƙaramar hukumar Zuru a Jihar Kebbi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar harin, inda ta bayyana cewa jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun yi nasarar fatattakar maharan a hare-hare biyu da suka kai a jere.
Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya ce maharan sun fara ƙoƙarin tare hanya ne a mahadar Rambo Junction da ke kan hanyar Ribah zuwa Dirin Daji da misalin ƙarfe 7:25 na yammacin ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai sun tunkari maharan, inda suka yi musayar wuta da su tare da tilasta musu ja da baya.
Sai dai, a cewarsa, maharan sun sake haɗuwa da dawowa cikin al’ummar, inda suka riƙa harbe-harbe daga wurare daban-daban.
A yayin musayar wutar, harsashi ya samu wani mai gadi mai shekaru 47 mai suna Hassan Boder, wanda ke aiki a wani sabon gidan mai da aka gina a kan hanyar Ribah zuwa Kanya, inda ya mutu.
Rundunar ’yan sandan ta ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da gudanar da sintiri domin kamo waɗanda suka aikata laifin.
Sai dai wasu rahotanni daga al’ummar yankin sun nuna cewa maharan, waɗanda suka zo kan babura sama da 10, sun yi awon gaba da wata matar aure a yayin harin.
Sojoji sun kuɓutar da mutum 11 da aka yi garkuwa da su
A wani labarin makamancin haka, dakarun Operation Fansan Yamma sun kuɓutar da mutum 11 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan soji guda biyu da suka gudanar a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi.
An gudanar da ayyukan ne a ranakun 30 da 31 ga Oktoba, 2026, bayan samun rahotannin hare-haren ’yan bindiga da ’yan ta’adda a yankin.
Kakakin runduna ta 8 ta sojoji da ke Sakkwato, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce aikin farko ya biyo bayan kiran gaggawa da aka samu cewa wasu ’yan bindiga sun tare hanya zuwa garin Ribah tare da ƙoƙarin kai hari ga al’ummar.
A cewarsa, bayan isa wurin, dakarun sun gano cewa an sace wasu mazauna yankin, sannan aka ga wasu babura da aka bari a wurin.
Ya ce sojojin sun bi sawun maharan tare da yin musayar wuta da su, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutum bakwai da suka yi garkuwa da su.
Mutanen da aka kuɓutar sun haɗa da Sa’adu Bala, Dantani Yahyi, Nura Musa, Nasiru Muhammad, Abdulakeem Abubakar, Abdulahi Maikudi da Zaki Gom.
Sanarwar ta ce an mayar da mutanen ga iyalansu.
A wani aikin kuma da aka gudanar a kusa da Wasagu, dakarun da ke sintiri sun fuskanci harin wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne, amma suka yi nasarar fatattakar su.
A yayin artabun, maharan sun tsere tare da barin mutum huɗu da suka yi garkuwa da su a gonakinsu da ke ƙauyen Wasagu.
Mutanen da aka kuɓutar su ne Lawali Ali, Samaila Shuaibu, Kasimu Shuaibu da Aliyu Bala, waɗanda duk mazauna ƙauyen Wasagu ne.
Daga bisani, sojojin sun miƙa su ga shugaban al’ummarsu.
Rundunar sojin ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyuka domin yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.