
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka manyan ’yan ta’addar ISWAP guda huɗu, ciki har da Larabawa biyu, wani kwamanda da wasu mayakan ƙungiyar a ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun haɗin gwiwa na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas ne suka hallaka mayakan a ranar 31 ga Oktoba, 2026, bayan wani kazamin artabu da suka yi da ’yan ta’addar a yankin.
Mukaddashin jami’in yaɗa labaran rundunar Operation Hadin Kai ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce dakarun sun yi amfani da ƙarfin sojin ƙasa da na sama, ciki har da jiragen yaƙi, wajen kai farmakin.
Sanarwar ta bayyana cewa cikin waɗanda aka hallaka akwai Abu Hajara, wanda ke cikin majalisar Shura ta ƙungiyar ISWAP, da Abul Walid, wani babban kwamanda kuma makusancin Ba Shuwa, wanda shi ne babban shugaban ISWAP (Wali).
Sauran biyun da aka hallaka kuwa manyan mayakan Larabawa ne da ke cikin ƙungiyar.
Kyaftin Goni ya ce bayan artabun, dakarun sun ƙwato makamai da alburusai masu yawa, da kuma na’urorin sadarwa daga hannun ’yan ta’addar.
Ya bayyana nasarar a matsayin wata babbar illa ga shugabanci da ƙarfin ayyukan ƙungiyar ISWAP, yana mai cewa hakan ya nuna ƙwarewa da shirin ko-ta-kwana na dakarun Operation Hadin Kai.
Sanarwar ta ƙara da cewa harin da ’yan ta’addar suka kai wa sansanin sojojin da ke Kukawa ya faru ne kwanaki uku kacal bayan wani farmaki a Buni Yadi, inda sojoji suka ce sun hallaka ’yan ta’adda 55, ciki har da wasu manyan kwamandoji.
Daga cikin kwamandojin da aka bayyana sunayensu akwai Ali Mandara Abba Gajiri, wanda aka fi sani da Munzir, da Habu Ikkima Nakif Yana Faruk, da kuma Kwamanda Gogore.
Rundunar ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da kare fararen hula masu bin doka da oda, tare da gudanar da ayyukan soji har sai an kawar da ’yan ta’addar da sansanoninsu a yankin.