Gobara Ta Lalata Gine-gine 75 da Rumfunan Kasuwa 35 a Kasuwar Katako ta Kano

Muhammadu SabiuHausa27 minutes ago



Wata gobara ta tashi a Kasuwar Katako ta Kofar Ruwa da ke Jihar Kano, inda ta lalata gine-gine na dindindin guda 75 da kuma rumfunan wucin gadi guda 35.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, PFS Kabiru Isah Jafaru, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 7:39 na safiyar ranar Asabar, bayan hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani ɗan kasuwar katako mai suna Alhaji Abba.

A cewarsa, a lokacin da hukumar ta samu kiran, ta tattara jami’an kashe gobara daga tashoshinta daban-daban da ke cikin birnin Kano tare da tura su zuwa wurin da lamarin ya faru.

Jafaru ya ce lokacin da jami’an suka isa kasuwar, gobarar ta riga ta bazu zuwa sassa daban-daban na kasuwar.

Ya bayyana cewa gobarar ta lalata gine-gine 75 na dindindin da kuma rumfunan wucin gadi 35.

Sai dai ya ce jami’an kashe gobarar sun samu nasarar shawo kan lamarin tare da hana wutar bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar.

Jami’in ya yi kira ga ’yan kasuwa da masu sana’o’i da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da ɗaukar matakan kariya daga gobara, musamman a lokacin ƙura da hazo (Harmattan).

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...