
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a mutuwar wasu yara biyu a ƙananan hukumomin Alkaleri da Ganjuwa na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce kamen ya biyo bayan wasu al’amura guda biyu da suka shafi mutuwar wani yaro mai shekara shida da wata yarinya mai shekara biyar.
A cewar sanarwar, lamarin farko ya faru ne a ranar 16 ga Oktoba, 2026, a ƙauyen Kwaimawa da ke ƙaramar hukumar Alkaleri, inda ake zargin wata uwar ɗaki mai suna Fatima Ibrahim, mai shekara 23, ta ba Mubarak Ibrahim, mai shekara shida, wani abin sha.
Sanarwar ta ce yaron ya fara yin amai ba kakkautawa jim kaɗan bayan shan abin, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Firamare da ke Kwaimawa, kafin daga bisani a mayar da shi Babban Asibitin Tarayya na Gombe domin ƙarin kulawa.
Sai dai, duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto rayuwarsa na tsawon kwanaki takwas, likita ya tabbatar da rasuwarsa a ranar 24 ga Oktoba, 2026. Rundunar ta ce an kama Fatima ne bayan shugaban ƙauyen ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda, kuma tana tsare yayin da ake ci gaba da bincike.
A wani lamari na daban, rundunar ta ce an tsinci gawar wata yarinya mai shekara biyar, mai suna Habiba Abubakar, a cikin wani ramin ruwa da ke bayan ƙauyen Badaromo, a ƙaramar hukumar Ganjuwa, da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar 24 ga Oktoba.
Kafin gano gawar, kakanta ya kai rahoton ɓacewarta ga ’yan sanda da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar 23 ga Oktoba, lamarin da ya sa mazauna yankin suka fara neman ta. Bayan gano gawar, jami’an ’yan sanda daga sashen Soro sun kewaye wurin tare da kama Sadiku Musa, mai shekara 19, bisa zargin hannu a mutuwarta.
Rundunar ta tabbatar da cewa an miƙa dukkan shari’o’in biyu ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Bauchi domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayyana rasuwar yaran a matsayin abin alhini da rashin tausayi, tare da tabbatar wa iyalan yaran cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da adalci.
Ya kuma jajanta wa iyalan mamatan, tare da kira ga iyaye, masu kula da yara da shugabannin al’umma da su ƙara kula da tsaron yara domin kare su daga duk wani haɗari.