EFCC Ta Kama ’Yan China 14 Da Dan Najeriya Kan Sarrafa Lithium Ba Bisa Ka’ida Ba



Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Zamba a Najeriya (EFCC) ta kama ’yan ƙasar China 14 da wani ɗan Najeriya guda ɗaya a wasu masana’antun sarrafa dutsen lithium guda huɗu da ake zargin suna aiki ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere, Jihar Ogun.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin ta shafinta na X, inda ta ce jami’an sashen gudanarwarta na Lagos Zonal Directorate 2 ne suka gudanar da samamen, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma sanya ido kan wuraren.

A cewar EFCC, an kama mutanen ne ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, yayin da ake gudanar da aikin sarrafa lithium a wuraren da ake zargin ba su da izinin yin hakan.

Hukumar ta ce jami’anta sun kwato buhunan duwatsun lithium, wayoyin hannu guda 18, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda huɗu, na’urorin decoders guda biyu, na’urar sarrafa talabijin da kuma babbar motar dakon kaya (trailer truck).

EFCC ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Wannan kamen na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ayyukan da ake zargin suna karya dokoki a sassa daban-daban na tattalin arziki, ciki har da haƙar ma’adanai da sarrafa su.

A watan Mayun 2026, an kuma gano wata maɓoyar masana’antar ƙera methamphetamine a cikin daji a Jihar Ogun, inda aka kama wasu ’yan ƙasar Mexico da kuma ’yan Najeriya. Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta bayyana samamen a matsayin mafi girman cafke methamphetamine da aka taɓa yi a wata masana’anta ta ɓoye a tarihin Najeriya.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...