EFCC ta bankaɗo haramtattun wurare 4 da ake sarrafa ma’adanin Lithium a Ogun

Jami’an hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati  sun samu nasarar kama wasu ƴan ƙasar China su 14 da wani ɗan Najeriya guda ɗaya a jihar Ogun.

Jami’ai daga ofishin hukumar ta EFCC shiyar Lagos ne suka samu nasarar kama mutanen a wasu haramtattun wurare huɗu da ake sarrafa ma’adanin Lithium a yankin Ogere na jihar Ogun.

An kama mutanen ne a ranar Juma’a 23 ga watan Oktoba biyo bayan gamsassun bayanan sirri da aka tattara akansu.

Bayan da  suka shiga hannu an same su da buhunan ma’adanin Lithium, kwamfutar laptop guda huɗu, motar tirela da sauran kayayyaki.

Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala gudanar da bincike.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...