An kama mutane biyu masu fashin manyan motoci a jihar Kogi

Sulaiman SaadArewa, Hausa13 minutes ago

Jami’an Tsaron  Aikin Sa-kai  na Jihar Kogi (KSVS) sun kama wasu mutum biyu da ake zargi mambobin wata ƙungiyar masu satar manyan motocin dakon kaya da kuma kayayyakin kamfanonin gine-gine ne.

Mai magana da yawun ƙungiyar bijilante ta KSVS Idris S. Idris, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai a ranar Litinin a Lokoja, inda ya ce jami’an bijilante na Zariagi ne suka samu nasarar  kama mutanen.

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun haɗa da Idris Muhammed mai shekaru 38 da Musa Muktar mai shekaru 33.

Ya ce an kama su ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, bayan makonni biyu ana tattara bayanan sirri da bincike. Ya ƙara da cewa sauran mambobin ƙungiyar sun tsere bayan musayar wuta da jami’an tsaro, amma sun samu raunukan harbin bindiga.

“Mutanen biyu sun yi musayar wuta da jami’an tsaro yayin da suke ƙoƙarin kwashe kayayyakin da suka sata ta amfani da babur mai taya uku (keke Napep). Tun daga nan suka amsa laifin da ake zarginsu da shi,” a cewar Idris.

Sai dai babban kwamandan KSVS, Alhaji Ibrahim Usman Anataku , ya buƙaci jama’a da su sanya ido kan duk wanda suke zargin yana da raunukan harbin bindiga tare da kai rahoto ga ofishin tsaro mafi kusa.

Anataku ya kuma yi kira ga jama’a da su ba da sahihan bayanan sirri ga jami’an tsaro, yana mai tabbatar musu da cewa za a kiyaye sirrin masu ba da bayanai da kuma bayanan da suka bayar.

Ya yaba wa gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo  bisa ci gaba da ba da goyon baya da ƙarfafawa da yake bawa  hukumar, sannan ya jinjinawa jami’ansa saboda ƙwazonsu da jajircewarsu wajen aiki.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...