NDLEA Ta Kama ’Yar Afirka Ta Kudu Da Hodar Iblis Mai Nauyin Kilogiram 36.65 A Filin Jirgin Saman Legas



Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar Afirka ta Kudu mai shekaru 34, Qhina Beauty, da hodar iblis mai nauyin kilogiram 36.65 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Hukumar ta kuma kama wata Ba’amurkiya ’yar asalin Najeriya mai shekaru 62, Anetor Gloria Ubong, da ake zargi da shigo da tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira loud, mai nauyin kilogiram 9.45 daga Amurka.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce kamen ya biyo bayan jerin samamen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da hukumar ta gudanar a jihohi daban-daban.

A cewar sanarwar, an kama Qhina ne a ranar 7 ga Oktoba, 2026, yayin da take shirin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Afirka ta Kudu ta Doha. Binciken jakunkunanta biyu ya gano tubalan hodar iblis guda 30, waɗanda aka ɓoye tare da busasshen barkono, aka naɗe su da leda, sannan aka tattara su cikin kunshe-kunshe bakwai.

Wadda ake zargin ta shaida wa jami’an hukumar cewa ta shigo Najeriya ne a ranar 30 ga Satumba domin karɓo kayan, bayan wata ’yar Afirka ta Kudu ta ɗauke ta aiki tare da yi mata alƙawarin biyan rand 20,000 idan ta kai kayan inda aka nufa.

Binciken da hukumar ta gudanar ya kai ga kama wani dillalin motoci mai shekaru 46, Uchenna Victor Umunnakwe, a ranar 14 ga Oktoba a yankin Apple Junction, Ago Palace Way, Legas. A cewar NDLEA, mutumin ya amsa cewa shi ne ya karɓi Qhina a filin jirgin sama, ya sauke ta a otal ɗin Santiago da ke Amuwo-Odofin, sannan ya mayar da ita otal ɗin Cynarisso kusa da filin jirgin kafin tafiyarta.

A wani samame na daban, hukumar ta kama Anetor Gloria Ubong a ranar 21 ga Oktoba, bayan ta isa filin jirgin saman Legas daga Houston, Amurka, a jirgin United Airlines. An gano kunshe-kunshe 18 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 9.45 a cikin akwatunanta biyu, waɗanda aka ɓoye da takardun naɗe kyaututtuka.

Ubong ta shaida wa jami’an cewa ’yarta da wanda zai zama surukinta ne suka kai mata akwatin a gidanta da ke Texas domin ta kai wa angon ’yarta mai suna Jibola a Najeriya.

Baya ga kamen da aka yi a filin jirgin sama, NDLEA ta ce jami’anta sun gudanar da wasu samame a jihohin Legas, Delta, Kano, Taraba, Neja, Bauchi, Ondo, Edo da Oyo, inda suka kwato miyagun ƙwayoyi da magungunan da ake amfani da su ba bisa ƙa’ida ba.

Daga cikin abubuwan da aka kwato akwai ƙwayoyin tramadol, diazepam da Rohypnol, kwalaben maganin tari mai ɗauke da codeine, alluran pentazocine da kuma manyan adadin tabar wiwi. A jihar Bauchi, an kama Jamilu Mustapha, wanda aka fi sani da Last Card, da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 379 a garin Nasaru da ke ƙaramar hukumar Ningi.

Haka kuma, hukumar ta ce ta gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 583 da aka bari a cikin buhuna 56 a wani farm da ke Board-Ala, ƙaramar hukumar Akure ta Kudu a jihar Ondo. A jihar Edo kuwa, jami’an hukumar sun lalata gonakin tabar wiwi guda biyu, tare da ƙiyasta yawan amfanin gonakin da ya kai kilogiram 2,023.14.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu, tare da kira gare su da su ci gaba da yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye a faɗin ƙasar.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...