

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce mafarauta masu taimaka wa al’umma sun kashe wasu mutum 14 da ake zargi ‘yan bindiga ne waɗanda suka shirya yin garkuwa da jama’a da yawa a ƙauyen Gidan Wawo da ke ƙaramar hukumar Bakori.
A cikin wata sanarwa, Nasir Danmusa, Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida ya ce an kashe ‘yan bindigar ne bayan da aka dakile harin da suka shirya kai wa ƙauyen.
Danmusa ya ce bayanan sirri da aka samu da misalin ƙarfe 1:28 na dare a ranar Juma’a sun nuna cewa ‘yan bindiga 26 masu ɗauke da manyan makamai, dake kan babura 13, suna kan hanyarsu ta zuwa dajin Dawan Laila domin shirya hare-hare a ƙauyukan da ke makwabtaka.
Ya ce Isiya Kwashen Garwa, wanda ake zargin fitaccen jagoran ‘yan bindiga ne, shi ne ya jagoranci mutanen.
Kwamishinan ya ce nan da nan jami’an tsaro suka sanya dukkan kayan aikinsu da dakarunsu a yankin Bakori cikin shirin ko-ta-kwana, lamarin da ya hana aiwatar da shirin yin garkuwa da mutanen.
Ya ƙara da cewa a wannan rana ne kuma ‘yan bindigar suka tare wata motar gida da ke ɗauke da fasinjoji huɗu daga mazabar Kakumi akan hanyarsu ta zuwa kasuwar Illela ta jihar Sakkwato, sannan suka ƙona motar.
Danmusa ya ce an tattara mafarauta daga Gidan Wawo, waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar da suka fara tserewa a wata musayar wuta.
Ya ce mafarautan sun kuma ceto fasinjoji uku da rai.
Kwamishinan ya bayyana cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar Mohammed Jidda, ɗaya daga cikin mafarautan , da kuma Jamilu Lawal, wani fasinja wanda ya mutu sakamakon ƙonewar da ya samu a gobarar motar.
Ya ce wani mafarauci kuma ya samu ƙananan raunukan harbin bindiga, kuma a halin yanzu yana karɓar magani.
Danmusa ya ce rahotannin sirri sun nuna yiwuwar ‘yan bindigar su ɗauki matakin ramuwar gayya bayan asarar da suka yi.
Ya ƙara da cewa an riga an ɗauki matakan kariya tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin hana duk wata barazana a gaba.