
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun ce sun kashe ’yan ta’adda 15 a wani harin sama da suka kai a arewa maso yammacin Pulka, da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:50 na daren 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da tabbatar da motsin ’yan ta’addan a yankin.
Kakakin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce bayan harin saman, sojoji sun kuma gudanar da aikin ƙasa domin bincika yankin da kuma ƙarfafa nasarar da aka samu.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda domin dakile ayyukansu da kare al’ummomin yankin.
Goni ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani motsi ko aikin da ake zargi, domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.