

Mutane biyar sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a babbar hanyar Obajana zuwa Lokoja a jihar Kogi.
An ruwaito cewa mutane biyar sun rasa rayukansu yayin da mutum guda ya samu munanan raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Obajana zuwa Lokoja a jihar Kogi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, lokacin da manyan motoci uku suka ƙwace saboda gudun wuce kima, suka yi karo da juna.
A cewar mazauna yankin, karon ya haddasa tashin gobara, lamarin da ya sa motocin da kayayyakin da suke ɗauke da su suka ƙone ƙurmus.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya ce manyan motoci uku sun yi karo da juna ne a ranar Lahadi 18/10/2026 da misalin ƙarfe 2:30 na dare a kan hanyar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar, mutum guda ya ji rauni, yayin da wani kuma bai samu wata illa ba.
Ya danganta musabbabin hatsarin da gudun wuce kima, wanda ya sa direbobin suka rasa ikon sarrafa motocin.
“An garzaya da wanda ya ji rauni zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Lokoja domin samun kulawa, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin adana gawa na asibitin.”