
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da sayen ƙarin motocin jirgin ƙasa da kayan aikin tsaro domin inganta harkokin sufurin jiragen ƙasa da kuma yaƙi da ayyukan ’yan bindiga, satar mutane da lalata kayayyakin more rayuwa.
Amincewar ta haɗa da sayen ƙarin motocin jirgin ƙasa domin ƙara yawan fasinjoji da kayayyakin da ake jigilarwa, tare da samar da na’urorin sa ido da za su taimaka wajen kare hanyoyin jirgin ƙasa da fasinjoji.
Babban sakatare a Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Funso Adebiyi, ne ya bayyana hakan ranar Asabar yayin duba aikin layin dogo na Kano zuwa Maradi.
Adebiyi ya ce ma’aikatar tana kuma horas da ma’aikatan jirgin ƙasa domin su iya sarrafa sabbin motocin da kuma kula da su bayan isowarsu.
Ya bayyana cewa rashin tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale ga harkokin sufurin jiragen ƙasa, saboda hare-hare kan kayayyakin more rayuwa na kawo tsaiko ga ayyuka, jefa rayukan jama’a cikin haɗari da kuma ƙara kuɗin gyara.
Ya kawo misali da hanyar jirgin ƙasa ta Abuja zuwa Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fuskanci barazanar tsaro.
“Na yi farin cikin sanar da ku cewa Shugaban Ƙasa ya amince mu fara sayen na’urorin sa ido da kayan aikin tsaro domin amfani da su a faɗin ƙasar nan, kuma muna aiki dare da rana domin tabbatar da hakan,” in ji shi.
A yayin ziyarar, Adebiyi ya samu rakiyar Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Sufuri da Zirga-zirga, Prince Adetokunbo Ademola Ade-John, da sauran jami’ai. Sun kuma duba aikin gina wani ɓangaren gada a kan hanyar layin dogon.