

Tsohon gwamnan jihar Delta, ya rasu yana da shekara 71.
Uduaghan, wanda ya yi wa’adin mulki biyu a matsayin gwamnan Delta tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015, ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya.
TheCable ta fahimci cewa ya rasu ne a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, kwanaki uku kacal kafin cikarsa shekara 72 a duniya.
An sanar da rasuwarsa ne a cikin wata sanarwa da iyalansa suka fitar, wadda Toju Anire ya sanya wa hannu.
“Zuukatanmu cike da bakin ciki da alhini mai girma, muna sanar da rasuwar ƙaunataccen mahaifinmu, ɗan’uwanmu, kawunmu kuma jagoran iyalinmu, Mai Girma Dakta Cif Emmanuel Eweta Uduaghan, tsohon gwamnan jihar Delta, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a safiyar ranar 19 ga Oktoba, 2026.” A cewar sanarwar
Sanarwar ta ƙara da cewa “Rasuwarsa ta girgiza mu matuƙa. Kalaman bakin ciki ba za su iya bayyana girman wannan rashi ba. Ya kasance mutum mai muhimmanci ga iyalinmu, kuma rayuwarsa da hidimarsa sun taɓa rayukan mutane marasa adadi a jihar Delta da ma Najeriya baki ɗaya.
Ya kasance ginshiƙi na ƙarfi, uba ga mutane da dama, ɗan’uwa abun ƙauna,kawu, kuma dattijo mai daraja. Za mu yi kewarsa ƙwarai, kuma za mu ci gaba da tuna kyawawan abubuwan da ya bari da kuma gadon alherinsa.”
An haifi Uduaghan ne a ranar 22 ga Oktoba, 1954. Ya yi aiki a matsayin kwamishinan lafiya na jihar Delta tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003.
Daga bisani, an naɗa shi sakataren gwamnatin Jihar Delta daga shekarar 2003 zuwa 2007.