Gwamnatin tarayya za ta fara sayar da kadarorin gwamnati a 2026

Ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya ta shirya fara sayar da kadarorin gwamnati ga ƴan kasuwa masu zuba jari a a shekarar 2026.

A cewar jaridar kasuwanci ta Bloomberg,Edun ya bayyana haka ne ranar Litinin a kasar Saudiyya wurin taron kasuwanci a kasashe masu tasowa.

Ya ce yanzu haka gwamnatin na aikin tabbatar da kadarorin da ya kamata a sayar da kuma tsawon lokacin da za a dauka kafin kammala cinikin.

” Shirin shi ne na sayar da wasu kadarorin a shekarar 2026,” ya ce.

More from this stream

Recomended