Ƴanbindiga sun yi garkuwa da fasinjoji a Neja

An yi garkuwa da mutane 20 yayin da suke tafiya a kan hanyar da ke haɗa Mariga da Kontagora a jihar Neja.

Fasinjojin na cikin tafiyarsu ne a kan hanyar lokacin da ‘yan fashin suka kafa shingen hanya suka kuma tilasta su shiga daji kusa da su.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkin-Daji, wanda ke wakiltar Mazabar Mariga, ya tabbatar da sace mutanen a ranar Alhamis.

Ya yi wannan bayani bayan da sojoji suka musanta ayyukan ‘yan fashi a filin horaswar sojoji da ke Mariga da Kontagora.

A cikin hirarsa da manema labarai, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da ‘yan fashin suka tare hanyar Mariga-Kontagora tsakanin Baban-Lamba da Beri.

More from this stream

Recomended