Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana’anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai.
Masana’antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kashe mayaƙan ƙungiyar da dama a yayin da sojoji suke ƙoƙarin ƙwace masana’antar.
Ya ce sojoji na musamman da hadin gwiwa jami’an Civilian JTF dake aiki ƙarƙashin rundunar Operation Desert Sanity III wacce ɓangare ne na rundunar Operation Haɗin Kai na cigaba da samun gagarumar nasara a ƙoƙarin su na ganowa tare da tarwatsa maɓoyar ƴan ta’addar a yankunan Talala, Gorgi, BUK da kuma jejin Sambisa
Bayanan da ya wallafa sun ce sakamakon ƙarfin bindigun sojoji ta tilastawa ƴan ta’addar tserewa domin a mafaka a wasu yankunan.