Kotun laifukan lalata da cin zarafin cikin gida a jihar Legas da ke zamanta a Ikeja a ranar Talata ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga daraktan kula da lafiya na gidauniyar kula da cutar daji, Dakta Olufemi Olaleye, bisa laifin lalata da ‘yar uwar matarsa.
Mai shari’a Rahman Oshodi ya yanke masa hukuncin ne bayan ya same shi da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 15.
Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun iya tabbatar da karar ba tare da wata shakka ba, kuma dukkan shaidun da ke gaban kotun sun tabbatar.
An gurfanar da Olaleye ne a kan laifuka biyu da suka shafi lalata da kuma cin zarafi ta hanyar lalata da ‘yar uwar matarsa.