Ƴan majalisa sun nemi a dakatar da Nigeria Air

Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama ya bukaci gwamnati da ta dakatar da kafa kamfanin Najeriya Air.

Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne a ranar Talata bayan wani bincike da aka gudanar kan kamfanin jirgin.

Idan dai za a iya tunawa tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya kaddamar da kamfanin jirgin ne jim kadan kafin ya bar aiki.

Sai dai a zaman da kwamitin ya gudanar ya gano cewa har yanzu kamfanin jirgin bai samu amincewar da ya kamata ba kafin kaddamar da shi.

More from this stream

Recomended