An bawa Iyalan wadanda suka mutu a harin jirgin kasar Kaduna tallafin miliyan 18

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayar da tallafi naira miliyan 18 ga iyalan mutane 9 da suka mutu a harin da aka kai kan jirgin kasar da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Iyalin kowane mamaci sun samu zunzurutun kuɗi har naira miliyan biyu.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna,KAD-SEMA,Muazu Mukaddas shi ne ya mika kudaden ga iyalan mutanen a wani taro da aka gudanar a Kaduna

Related Articles