Jami’an rundunar ‘yan sanda ta Jihar Anambra sun kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane, wanda ake zaton yana addabar mazauna yankin hanyar Enugwu-Ukwu a karamar hukumar Njikoka ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar cewa jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin bayan musayar wuta tsakaninsu da ‘yan kungiyar.
Ikenga ya ce jami’an tsaro sun samu wannan nasara ne bayan samun sahihan bayanai kan ayyukan kungiyar, inda suka dakile shirinsu ta hanyar kai dauki cikin gaggawa.
Ya ce, “A ranar 22 ga watan Nuwamba, 2024 da misalin ƙarfe 10:30 na safe, haɗin gwiwar jami’an tsaro daga ‘yan sanda da ‘yan bijilante na Anambra sun kashe wani mamba na wata ƙungiyar ‘yan fashi da ke aiki a hanyar Nkwo Enugu-Ukwu. An kuma kwato bindiga kirar AK-47 ɗaya, mujallu biyu, da harsashi masu rai guda biyar.”