Tinubu Ya Naɗa Matashi a Matsayin Sabon Shugaban JAMB

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB.

Aina mai shekaru talatin da tara zai maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar talatin da ɗaya ga watan Yulin shekarar dubu biyu da ashirin da shida.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana sabon shugaban a matsayin ƙwararren masani mai gogewa a harkokin jarrabawa, fasahar intanet da sauye-sauyen al’umma.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]