Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jigo a jam’iyar APC

Yan bindiga sun yi garkuwa da Kawu Yakasai jami’in tsare-tsare na jam’iyar APC a jihar Kaduna.

An ce an yi awon gaba da Yakasai ne ranar Juma’a da daddare a karamar hukumar Soba ta jihar.

Kawo yanzu yan bindigar ba su bukaci a biya su kudin fansa ba ko kuma tuntubar iyalinsa.

Da yake ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar, Muhammed Shehu babban jami’in yada labarai na gwannan jihar Uba Sani ya ce tuni gwamnan ya bada umarnin jami’an tsaro su zakulo masu garkuwar su kuma kuɓutar da Yakasai.

Shehu ya ce gwamnatin jihar Kaduna na aiki domin daukar yan bijilante 7000 domin taimakawa kokarin da jami’an tsaro su ke yi.

More from this stream

Recomended