
A ƙalla mutane huɗu aka kashe bayan da wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kai hari kan kauyen Giyawa dake karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto.
A cewar Ahmad Rufa’i mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane 18.
Rufa’i ya kara da cewa 7 daga cikin mutanen da aka sace sun kubuta inda suka dawo kauyen.
Ya kuma kara da cewa jami’in tsaro na bin sawun yan bindigar.
Jihar ta Sokoto na daga cikin jihohin da suke yankin arewa maso yamma dake fama da hare-haren yan bindiga.