
Ƴan bindiga sun harbe wani manomi tare da sace karin wasu mutane 7 ;maza biyu mata biyar a kauyen Unguwar Gajere dake mazabar Kutemeshi a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
An kai wa mutanen farmaki ne lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar 2 ga watan Agusta.
Mamba mai wakiltar mazabar, Kakangi a majalisar dokokin jihar, Yahaya Musa shi tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yan bindigar sun kuma sace dabbobi a kauyukan dake kusa da garin.
A cewar sa halin da ake ciki abun damuwa ne sosai inda ya jajantawa iyalan da suka yi asarar rayukan yan uwansu.
Ya ce yawanci yan bindigar suna satar shanu a kauyukan Gwandu da Damari.
Wan mazaunin kauyen ya ce kauyukan suna yawan fuskantar hare hare daga yan bindigar inda ya ce kisan na neman zama abin dake faruwa kullum. Ya yi kira da akawo musu dauki daga hukumomin da abin ya shafa.