Yadda aka sace wanda ya kai kudin fansa a Kaduna | BBC Hausa

Jihar Kaduna na fama da matsalar satar mutane
Image caption

Kungiyar al’ummar Zuru mazauna Kaduna ta tabbatar da sace wasu ‘ya’yanta malaman jami’a guda biyu, inda ta ce masu garkuwar sun bukaci sai an biya kudin fansa kafin sakin su.

Bayanai sun ce an fara sace na farkon ne, tun ranar Alhamis, kafin mutanen da ke garkuwa da shi su sake kama kaninsa a lokacin da ya je domin ya karbo dan’uwansa a ranar Lahadi.

Wani na kusa da wadanda aka sacen ya ce tun farko an bukaci su biya kudi miliyan biyu da sabon babur kafin a saki wanda aka fara sacewa.

Ya ce bayan cika wadannan ka’idoji barayin sun bukaci cewa kanin wanda aka sace din ne zai kai kudin fansar da sauran kayan da suka bukata.

Sai dai bayan da kanin da kuma wasu mutane biyu masu rakiya suka isa bakin jeji, barayin sun bukaci su tafi da kanin wanda aka sacen domin ya taho da dan’uwansa, inda suka bukaci sauran masu rakiya biyu da su jira a bakin daji.

A cewar sa “Nan suka (masu rakiya) kwana har gari ya waye ba su ga dawowar dayan da aka shiga daji da shi ba.”

Ya kara da cewa “Da suka gaji shi ne suka dawo gida, suka ba mu labarin cewa sun jira ba su ga dawowar wancan ba, shi ya sa suka dawo gida.”

Ya tabbatar wa BBC cewa ba da dadewa ba ne sai suka samu kira daga barayin wadanda suka ce suna neman a biya makudan miliyoyin Naira kafin a karbo mutanen biyu.

Al’amarin shi ne na baya-bayan nan da aka samu labari a cikin jerin sace-sacen mutane domin neman kudin fansa da ya zama gagarumar matsalar tsaro a yankin Kaduna, duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...