Wata mata da ’ya’yanta sun tsallake rijiya da baya a jihar Jigawa bayan wata mota da ta sauka daga kan hanya ta kutsa kai cikin wani gida, lamarin da ya haddasa konewar gidaje hudu kurmus.
Hatsarin, wanda ya faru ranar Lahadi, ya tayar da hankulan mazauna yankin da ke kusa da titin.
Wata majiya ya shaida wa manema labarai cewa, “Motar ta kutsa kai cikin gidan har ta rushe bango sannan ta shiga ɗakin da matar tare da ’ya’yanta suke barci.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa, DSP Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi.
A cewarsa, matar da ’ya’yanta sun tsira daga hatsarin, amma gidaje hudu sun kone kurmus a yayin afkuwar lamarin.